Sanarwar da kungiyar ta fitar jiya, ta ce tawagar ta tattara wasu bayanai a garin Duma, ciki har da wasu sinadaran da ta gano a wurin, wadanda ta riga ta tura zuwa dakin gwaje-gwaje na kungiyar don gudanar da bincike, abun da zai dauki tsawon mako uku zuwa hudu.
A ranar 7 ga watan Afrilun bana ne, aka yi amfani da makamai masu guba wajen kai hari garin Duma dake yankin gabashin Ghouta na kasar Siriya, inda gwamnatin kasar ta musanta zargin da ake mata na kai harin, tare da gayyatar kungiyar OPCW don tura tawagarta zuwa garin Duma da nufin gudanar da bincike.(Murtala Zhang)