in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
John Kerry da shugaban Saudiyya sun tattauna batutuwan Siriya da yaki da ta'addanci
2016-05-16 09:42:05 cri
A jiya ne, John Kerry, ministan harkokin wajen kasar Amurka da ya ziyarci kasar Saudiyya, ya yi shawarwari da sarkin kasar Saudiyya Salman Bin Abdulaziz Al-saud, inda suka tattauna hadin gwiwar da ke tsakaninsu game da batun Siriya da yaki da ta'addanci.

Kafin wannan ziyara, Kerry ya bayyana cewa, makasudin ziyarar shi ne a daidaita matsayi tsakaninta da kasar Saudiyya game da batun Siriya da na yaki da ta'addanci, don ba da tabbaci game da ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka daddale tsakanin sojojin gwamnatin da bangaren 'yan adawa, da share fagen jigilar kayayyakin agaji, kana da farfado da yunkurin siyasa game da batun Siriya.

Bayan da Kerry ya kammala ziyararsa a Saudiyya, zai kuma yi tattaki zuwa birnin Vienna, don shirya taron kasa da kasa game da batun Siriya tare da takwaransa na kasar Rasha, wanda za a gudanar a ranar 17 ga wata, kuma taron da ake fatan kimanin kasashe 17 za su halarta.

Saudiyya ta kasance kasar da ke goyon bayan bangaren adawa na kasar Siriya, game da batun Siriya, kuma tana ganin cewa, ya zama dole shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad ya sauka daga mukaminsa, don a shirya zabe tare da kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkan kabilu daban daban na kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China