in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a bude filin jirgin saman Aleppo dake kasar Siriya
2016-12-22 10:49:57 cri

Mahukuntan kasar Siriya sun bayyana cewa, nan ba da jimawa ba, za'a sake bude filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Aleppo dake arewacin kasar Siriya.

Wani babban jami'in filin jirgin saman ya fadawa 'yan jaridu cewa, sojojin gwamnatin Siriya sun cimma manyan nasarori lokacin da suke gudanar da aikin soja a Aleppo, kuma za'a sake bude filin jirgin saman bayan da aka kammala aikin gyare-gyaren da aka yi masa.

Rahotanni na cewa, Aleppo ya taba zama birni mafi girma kana cibiyar tattalin arzikin kasar ta Siriya. A farkon shekara ta 2012 ne, yaki ya barke a Aleppo, inda sojojin gwamnatin Siriya suka mamaye yammacin birnin, yayin da 'yan tawaye kuma ke rike da gabashin birnin.

Shi dai wannan filin jirgin sama yana arewa maso gabashin birnin Aleppo, wanda ke karkashin ikon sojojin da ba sa ga-maciji da gwamnati cikin dogon lokaci. Kuma an dakatar da amfani da shi ne tun farkon watanni 6 na shekara ta 2013 sakamkon tabarbarewar yanayin tsaro.

Tun a watan Satumban shekarar da muke ciki ne, sojojin gwamnatin Siriya suka kara fatattakar 'yan tawaye, inda suka yi musu kawanya. Kwanan baya, sojojin gwamnati da 'yan tawaye sun cimma wata yarjejeniya, na nufin barin dakaru 'yan tawaye da aka yi musu kawanya a kudu maso gabashin Aleppo su janye daga birnin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China