in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harba makamin roka ofishin jakadancin Rasha dake kasar Siriya
2016-12-29 11:17:53 cri
Jiya Laraba 28 ga wata, ofishin watsa labarai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya sanar da cewa, har sau biyu, 'yan ta'adda sun harba makamin roka kan ofishin jakadancin Rasha dake kasar Siriya a birnin Damascus, lamarin da bai hallaka ko raunata wani ba.

An ce, daga misalin karfe 1 zuwa karfe daya da minti 19 na yammacin ranar, agogon Moscow, sau biyu a jere ne 'yan ta'addan suka harba rokoki kan ofishin jakadancin Rasha. Makaman roka sun fada cikin harabar ofishin jakadancin, amma ba su fashe ba, inda daga bisani, aka kawar da su.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, ofishin jakadancinta dake Syria, gami da jami'an diflomasiyya, sun dade suna fuskantar barazana daga wasu kungiyoyin 'yan ta'adda dake yankunan karkarar birnin Damascus.

A halin yanzu, akasarin yankunan karkara dake gabashin birnin Damascus na karkashin ikon dakarun da ba sa ga-maciji da gwamnati da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China