in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi shugabar majalisar dokoki ta farko a kasar Siriya
2016-06-07 14:01:06 cri
A ranar Litinin ne aka zabi Hadiyeh Abbas, a matsayin sabuwar shugabar majalissar dokokin kasar Siriya. Yanzu haka dai Hadiyeh ta zama 'yar majalisar dokoki ta farko da ta dare wannan kujera tun da aka kafa majalisar dokokin kasar a shekarar 1919.

An haifi Hadiyeh a lardin Deir Ez-Zor dake yankin gabashin kasar Siriya a shekarar 1958, kuma ta kammala karatu a jami'ar Aleppo. Kana ta samu digiri na uku a fannin aikin gona na zamani. Daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 ta zama 'yar majalisar dokoki.

An yi zaben majalisar dokokin dai a ranar 13 ga watan Afrilu, kuma 'yan takara sama da 3000 suka yi takarar kujeru 250 a majalisar dokokin kasar. Kawancen jam'iyyun dake karkashin shugabancin jam'iyyar ASRP ta sake samun nasara, inda ta samu kujeru 200, koda yake muhimmin bangarorin 'yan adawar kasar na gida da na waje sun kaurace zaben.

Bisa tsarin mulkin kasar, ana kada kuri'u a zaben majalisar dokokin kasar ne a ko wadannan shekaru hudu-hudu, kuma shugaban majalissar dokokin na da wa'adi na shekaru 4. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China