in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Ya dace a kara azama wajen gina kauyuka masu kyakkyawan yanayi
2018-04-23 11:18:53 cri

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da shirin shekaru 3 na kyautata yanayin zaman rayuwar jama'a dake yankunan karkara, da farfado da kauyukan, da koyi daga fasahohin lardin Zhejiang, da gina kauyuka masu kyakkyawan yanayi na zaman rayuwar jama'a.

A kwanakin bayan ne Xi Jinping ya bayyana hakan, yana mai cewa, ya kamata a kyautata yanayin kauyuka a yankuna masu arziki, da kuma yankuna marasa ci gaba, kuma ma'aunin hakan ya kamata ya dace da halin da suke ciki.

Bayan aiwatar da aikin kyautata yanayin kauyuka a shekarar 2003, an kyauatata yanayin kauyukan, da karfin tattalin arzikinsu, da zaman rayuwar jama'arsu a lardin na Zhejiang, matakin da ya sada al'ummar Sinawa da fasahohi a dukkan kasar ta Sin a fannonin gina kasa mai kyakkyawan muhalli, da farfado da kauyuka da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China