Shugaban na Sin ya bayyana hakan ne, yayin ziyarar da ya kai madatsar ruwa ta "Three Gorges" dake hade da kogin Yangtze, wadda ke kusa da birnin Yichang a lardin Hubei.
Da yake duba kayayyakin aiki a yankin masana'antu dake daura da kogin na Yangtze, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin hade burin ci gaban tattalin arziki, da bukatar kare muhallin halittu. Ya ce farfado da muhallin halittu shi ne kan gaba, kuma dole ne a kare wannan kogi yadda ya kamata. Ya kara da cewa ba za a taba amincewa da duk wani mataki da zai kai ga gurbata muhalli ba.
A matsayin sa na aikin dake samar da makamashin lantarki ta ruwa mafi girma a duniya, Dam din "Three Gorges" na samar da moriya mai tarin yawa. Rahotanni sun ce madatsar ruwan ta karade fili da ya kai tsayin mita 2,309, da tudun mita 185. Yana kuma samar da lantarki daga injuna 32. Kaza lika yana da wuraren turke jiragen ruwa da na daga su.(Saminu Alhassan)