in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: ya kamata a raya dangantaka tsakanin Sin da Indiya bisa manyan tsare-tsare
2018-04-28 16:39:10 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi jiya da yau a birnin Wuhan na lardin Hubei da ke kasar Sin, inda Xi ya nuna cewa, amincewar juna ita ce tushen raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Indiya. Ya ce ya kamata a raya dangantakar bisa mayan tsare-tsare, da kara fahimta da aminta da juna. Haka kuma ya kamata a yi kokari domin sassa daban daban na kasashen biyu da kuma jama'arsu, su kara fahimtar juna, da sada zumunta a tsakaninsu. Ya na mai cewa a nan gaba, Sin da Indiya za su tsara wani shirin hadin gwiwa daga dukkan fannoni.

Xi ya kuma jaddada cewa, ya kamata a mai da hankali kan batutuwa uku. Da farko, Sin da Indiya makwabta ne kuma aminai. A don haka, ya kamata a dauki juna a matsayin abokan da za su iya hadin kai don cimma burinsu na samun ci gaba. Na biyu, bunkasar huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta dace da zamanin da ake ciki, kuma muhimmiyar dama ce ga juna. Sannan na uku ya ce, Sin da Indiya dukkansu na tsayawa kan ra'ayin samun 'yancin kai, don haka ya kamata su yi nazari kan aniyar juna bisa ka'idojin nuna himma da bude kofa da hakuri da juna.

Har ila yau, Xi ya ce Sin da Indiya na daukar ra'ayi kusan iri daya a cikin wasu lamuran duniya. Yayin da take daidaita hulda da manyan kasashe, Sin na tsayawa kan ra'ayoyin cin gashin kai bisa manyan tsare-tsare, da rashin adawa da juna. Ko da yaushe ta kan nace ga ra'ayin raya sabuwar huldar girmama juna da tabbatar da adalci da hadin gwiwa don moriyar juna tsakanin kasa da kasa.

A nasa bangaren Mr. Modi ya furta cewa, a karni na 21, Indiya da Sin za su hada kansu domin bayar da babbar gudummawa ga zaman lafiya da zaman karko da wadatar nahiyar Asiya da ma duniya baki daya. Ya kuma yarda da cewa, Indiya da Sin za su rika tuntubar juna bisa manyan tsare-tsare. Ya ce akwai ra'ayi da kuduri da buri na bai daya wajen raya hular da ke taskanin kasashen biyu, don haka ya kamata su kara yin mu'amala da juna, da inganta hadin kansu, da kara fahimta da amincewar juna, kana da daidaita bambamce-bambance a tsakaninsu yadda ya kamata, domin raya dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China