in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Najeriya sun amince da musaya a fannin hada hadar kudi
2018-05-03 20:04:45 cri
Babban bankin kasar Sin PBOC, ya ce ya amince da wata yarjejeniya tsakanin sa da babban bankin Najeriya, wadda ta shafi musaya a fannin hada hadar kudade.

Yarjejeniyar dai za ta baiwa sassan biyu damar yin musayar kudade da suka kai Yuan biliyan 15, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.35, kan kudin Najeriya Naira biliyan 720 tsakanin shekaru 3 masu zuwa.

Wata sanarwar da babban bankin na Sin ya fitar kan shafin sa na yanar gizo, ta ce daukar wannan mataki na da nufin karfafa dangantakar cinikayya, da zuba jari, da daidaita yanayin hada hadar kudade tsakanin sassan biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China