Kafofin watsa labaran kasar sun rawaito gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa'i na cewa, shugaban kasar ya shaidawa wani taron shugabannin jam'iyyarsa ta APC wannan aniya tasa.
A wata zantawa da ya yi ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin shugaban kasar Garba shehu, ya tabbatar da wannan batu, yana mai cewa ko shakka babu shugaban Najeriyar ya bayyanawa 'yan jam'iyyar tasa, burin sa na tsayawa takara a babban zaben kasar dake tafe cikin farkon shekara mai zuwa.