in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane akalla 10 sun mutu yayin wani hari da 'yan bindiga suka kai yankin tsakiyar Nijeriya
2018-04-23 11:02:47 cri

Mutane akalla 10 sun mutu sanadiyyar wani hari da 'yan bindiga suka kai wa al'ummar manoma a jihar kogi dake arewa maso tsakiyar Nijeriya a jiya Lahadi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ali Janga, ya ce an tabbatar da mutuwar akalla mutanen yankin 5 da mahara 5.

Ali Janga ya ce an kashe maharan ne yayin musayar wuta da suka yi da jami'an tsaro bayan farwa garin Kpanche da suka yi.

Har ila yau, ya ce an kuma gano wasu makaman maharan, sannan an kone gidaje 5 da wasu ababen hawa da ba a san adadinsu ba da kuma wasu kadarori. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China