in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya gana da 'yan matan sakandaren Dapchi da aka sako
2018-03-24 13:53:21 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya karbi 'yan mata sakandaren Dapchi da 'yan Boko Haram suka sako a baya-bayan nan.

Muhammadu Buhari ya kuma roki iyayen 'yan matan sakandaren Chibok da har yanzu ba a sake su ba, da kada su yanke kauna, domin ana kara kaimi ga kokarin tabbatar da sakinsu.

Shugban ya bayyana haka ne a Abuja babban birnin kasar, yayin liyafar da aka shiryawa 'yan matan sama da 100 da wani yaro guda da 'yan ta'addan suka saki.

Jimilar 'yan mata 110 ne kungiyar Boko Haram ta sace daga kwalejin 'yan mata ta garin Dapchi dake arewa maso gabashin kasar a ranar 19 ga watan Fabrerun da ya gabata.

Rahotanni na cewa 'yan mata 104 ne aka mayar da su a ranar Laraba da ta gabata bayan cimma yarjejeniya. Sannan an saki wata yarinya da wani yaro tare da 'yan matan dalibai.

Shugaban ya kuma jadadda kudurin Gwamnatinsa na yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda. Inda ya ce tuni aka umarci hukumomin tsaro su dauki matakan da suka dace a dukkan makarantun da za a iya kai wa farmaki domin tabbatar da tsaron dalibai da malamai da ma'aikatan makarantun.

Har ila yau, Shugaba Buhari ya bukaci hukumomin tsaron su tabbatar da kasar ba ta sake fusknantar makamanci al'amarin ba. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China