Shugaban karamar hukumar Logo ta jihar, Richard Nyajo, ya ce wasu mutane sun farwa wata mujami'a da makarantar firamare a yankin, inda suka yi ta harbe-harbe.
A cewarsa, galibin wadanda harin ya rutsa da su na neman mafaka ne a mujami'ar da makarantar dake unguwar Mbamono, saboda harin da aka kai kafin na safiyar jiyan, ya raba su da matsugunansu, yana mai cewa mafi yawa daga cikinsu suna barci a lokacin da aka kai harin.
Har yanzu babu takamaiman adadin wadanda suka jikkata. Sai dai ya ce ana zargin makiyaya da kai harin.
Jihar Benue ta kasance a yankin tsakiyar Nijeriya, inda ta raba tsakanin yankunan arewaci da kudancin kasar. (Fa'iza Mustapha)