in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar wakilan Somalia ya yi watsi da bukatar ya sauka daga mukaminsa
2018-04-04 13:03:48 cri
Shugaban majalisar wakilan kasar Somalia Mohamed Osman Jawari, ya ce ba zai yi murabus ba kamar yadda ake matsa masa lamba daga majalisar zartarwar kasar, a daidai lokacin da aka tsaida yau Laraba a matsayin ranar da za a tafka muhawara kan kudurin tsige shi.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai a Mogadishu, Mohamed Jawari ya ce zaman da majalisar za ta yi yau, don tattaunawa game da dabi'unsa bai dace ba, kuma ya sabawa kundin tsarin mulki.

Shugaban wanda mambobin majalisar ke zargi da take kundin tsarin mulki, ya kuma zargi shugaban kasar Mohamed Farmajo da kara ta'azzara rikicin siyasa a kasar dake kahon Afrika, ta hanyar nemansa ya yi murabus, maimakon ya warware rikicin ba tare da goyon bayan wani bangare ba.

Kudurin tsige Jawari ya gaza tattaro isashen adadin mambobi 92 da ake bukata a ranar 15 ga watan Maris, bayan mambobin 16 sun janye goyon bayansu ga kuduri a matakin karshe.

An dage muhara kan kudurin tsigewar har sau 3, inda mambobi masu adawa da shugaban ke kokarin tattaro wadanda za su sanya hannu kan kudurin kada kuri'ar yanke kauna da shugaban na su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China