in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Uganda sun kashe mayakan Al-Shabaab 22 a Somalia
2018-04-02 11:15:37 cri

Rundunar tsaron UPDF ta Uganda, ta ce dakarunta sun kashe mayakan al Shabaab 22 jiya Lahadi a Somalia.

Wata sanarwa da kakakin rundunar UPDF Col. Deo Akiiki ya fitar, ta ce dakarun da aka tura Somalia karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika wato AMISOM, sun kashe 'yan ta'addan ne a lokacin da suke yunkurin kai hari kan sansanonin soji na Quoroyole da Buulo Mareer da Golwen dake yankin Lower Shabelle na Somalia.

Sanarwar ta ce an kashe sojojin UPDF 4 yayin da wasu 6 suka samu raunuka marasa tsanani yayin arangamar ta safiyar jiya.

Sanarwar ta kara da cewa, an lalata motocin 'yan ta'addan guda 8, ciki har da guda biyu dake dauke da bambamai, ya na mai cewa an kuma kwato nau'o'in bindiga daban-daban. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China