in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci kasashen duniya su tallafawa Somalia don ta samu karfin yakar barazanar ta'addanci
2018-04-19 10:31:53 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia (AMISOM), ya bukaci kasa da kasa da su tallafawa kasar Somalia domin ta samu kwarin gwiwar yakar barazanar ayyukan ta'addanci dake neman ta'azzara a kasar.

Wasu manyan jami'an shirin na AMISOM da suka hada da jami'an tsaro wadanda suka kammala taron karawa juna sani na shekara shekara karo na 4 game da batun kawar da abubuwan fashewa da suka gudanar a Mogadishu, sun cimma matsaya game da irin matakan da zasu dauka na dakile barazanar yaduwar ababen fashewa wanda ke zama a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar kasar.

A wata sanarwar hadin gwiwa da mahalarta taron shirin kungiyar ta AU ta fitar ta ce, daga cikin batutuwan da taron ya cimma matsaya kansu sun hada da yin amfani da hanyoyin kimiyya wajen bincike kan wadanda ake zargi da aikata laifuka da kuma bayar da ingantaccen horo ga jami'ai domin dakile barazanar ababen fashewa.

Taron dai ya yi amanna cewa yadda mayakan al-Shabab ke cigaba da amfani da ababen fashewa babu kakkautawa ya kasance a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta gabashin Afrika, kana taron ya jaddada aniyar daukar matakan da za su tabbatar da magance matsalar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China