in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin za ta rage rabin lokacin zartas da shirye-shiryen bude kamfani da kaddamar da ayyuka ko fiye da haka
2018-05-03 10:47:54 cri

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira taron mambobin dindindin na majalisar, inda ta tsai da kudurin daukar matakan rage fiye da rabin lokacin zartas da shirye-shiryen bude kamfani da kaddamar da ayyuka, a kokarin kara kyautata yanayin tafiyar da harkokin kasuwanci. Kana kuma an zartas da daftarin ka'idojin wucin gadi kan kasuwar ma'aikata.

Taron wanda ya gudana karkashin shugabancin Firaministan kasar Li Keqiang, ya yi nuni da cewa, dole ne a aiwatar da ayyukan tattalin arziki da kwamitin tsakiya na JKS ya tsai da a yi, da ayyukan da aka tanada cikin rahoton ayyukan gwamnatin, da zurfafa yin gyare-gyare kan yadda gwamnatin take kulawa da ayyuka da kyautata hidima, da daidaita batutuwan da suka shafi zartas da shirye-shiryen bude kamfani da kaddamar da ayyuka, alal misali, an sha fuskantar matakai da dama, kuma ana daukar dogon lokaci. Za a rage lokacin ne ta yadda za a amfana wajen rage kudin kashewa bisa tsare-tsare da kuma karfafa gwiwar al'umma wajen gudanar da harkoki da yin kirkire-kirkire. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China