in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Trump ya sanar da mambobin tawagar da za su tattauna batun cinikayya da kasar Sin
2018-05-01 16:13:15 cri

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa wata tawaga ta musamman ta kasar, za su zo kasar Sin, domin tattauna batun cinikayya tsakaninsu daga ranar Alhamis mai zuwa.

Mambobin tawagar sun hada da Jakadan Amurka a kasar Sin Terry Branstad da Sakataren Baitulmalin kasar Steven Mnuchin da Sakataren ma'aikatar cinikayya Wilbur Ross da kuma Robert Lighthizer, wakilin hukumar dake tsara manufofi da bada shawara ga shugaban kasar kan cinikayya.

A makon da ya gabata ne Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar Sin na girmama kudurin da Amurka ta nuna na magance takaddamar cinikayya tsakaninsu bisa tattaunawa da tuntubar juna.

Ya kara da cewa, babu wanda ke nasara a takaddamar cinikayya, wanda illarsa ba zai tsaya ga farfadowar tatalin arzikin duniya kadai ba, har ma da tsarin masana'antun duuniya, yana mai cewa ta hanyar tattaunawa ne kadai za a samu mafita.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Donald Trump ta yi barazanar kakaba haraji kan kayakin da kasar Sin ke shigarwa Amurka da kudinsu ya kai dala biliyan 150, yayin da kasar Sin ta lashi takobin daukar makamancin matakin kan kayakin da Amurka ke shigawar kasarta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China