in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin zai ziyarci Indonesia da Japan
2018-05-02 09:42:23 cri
Firaministan kasar Mista Li Keqiang zai kai ziyara kasar Indonesia, daga bisani kuma zai tafi kasar Japan domin ziyarar aiki da halartar taron shugabannin kasashen Japan, Koriya ta Kudu, da Sin karo na 7.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ce ta sanar da hakan a jiya Talata.

Mista Li zai gudanar da wadannan ayyuka ne tsakanin ranekun 6 zuwa 11 ga watan da muke ciki. Zai kai wannan ziyara ne bisa gayyatarsa da shugaban kasar Indonesia Joko Widodo da firaministan kasar Japan Shinzo Abe suka yi. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China