Ministan kudin kasar Amurka zai ziyarci kasar Sin
Manzon musamman na shugaban kasar Amurka, kana ministan kudin kasar Steven Mnuchin,zai jagoranci wata tawaga da za ta kawo ziyara kasar Sin tsakanin ranekun 3 zuwa 4 ga watan da muke ciki, inda mataimakin firaministan kasar Sin Liu He zai yi musayar ra'ayi da jami'an na Amurka, musamman ma a fannin batun cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ke jan hankalin bangarorin 2.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku