in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kuwait sun sha alwashin zurfafa hadin gwiwa da samun bunkasuwa ta bai daya
2018-04-30 16:26:11 cri
Wakilin shugaban kasar Sin wanda ke ziyarar aiki a Masarautar Kuwait Mr. Yang Jiechi, ya bayyana aniyar gwamnatin kasar Sin game da zurfafa hadin gwiwa, da samun bunkasuwa tare da kasar Kuwait.

Mr. Yang wanda ya zanta da Sarkin masarautar ta Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah a ranar Lahadi, ya ce sassan biyu za su dauki kwararan matakai na fadada kawance daga dukkanin fannoni.

Yang, wanda mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kuma darakta a ofishin lura da harkokin waje na kwamitin, ya mika sakon gaisuwar shugaba Xi ga masarautar Kuwait da ma daukacin al'ummarta.

Kuwait dai na cikin kasashen farko da suka sanya hannu kan shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, don haka a cewar Yang, Sin na daukar kasar a matsayin muhimmiyar kawa a fannin aiwatar da tanajin dake kunshe cikin wannan shawara tsakanin kasashen dake yankin Gulf.

A nasa bangaren, sarkin na Kuwait ya bukaci Mr. Yang da ya mika sakonsa na gaisuwa da fatan alheri ga shugaba Xi. Yana mai cewa Kuwait na daukar Sin a matsayin aminiya, kuma kawa ta hakika a fannin hadin gwiwa. Daga nan sai ya yi fatan dorewar dangantaka tsakanin kasar sa da Sin.

Ya ce Kuwait na fatan zurfafa hadin gwiwa da Sin a dukkanin fannoni, za kuma ta shiga a dama da ita, wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, tare da hade hakan da manufar ci gaba ta "biranen Siliki da tsibirai 5 ".

A shekarar 2013 ne dai kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, wadda aka yiwa lakabi da hanyar Siliki ta raya tattalin arziki ta kasa, da hanyar Siliki ta ruwa ta karni na 21, kudurin dake da nufin kafa tsarin ciniki da kasuwanci, dama samar da ababen more rayuwa da za su hade sassan nahiyoyin Asiya da Turai da Afirka, ta tsohuwar hanyar Siliki da aka taba amfani da ita.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China