in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da Jamhuriyar Dominica sun kulla dangantakar diflomasiyya
2018-05-01 15:52:23 cri

Kasar Sin da Jamhuriyar Dominica, sun rattaba hannu kan wata sanarwar a yau Talata, wadda ta bayyana kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu.

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma Ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi da takwaransa na Dominica Miguel Vargas ne suka rattaba hannu kan sanarwar.

A cewar sanarwar, gwamnatin Jamhuriyar Dominica ta amince da manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma gwamnatin jamhuriyar al'ummar kasar Sin ita ce halatacciyar gwamnati dake wakiltar baki dayan kasar, kana Taiwan, yanki ne na kasar Sin da ba zai iya ballewa ba.

Ta kara da cewa, a don haka, daga yau, Jamhuriyar Dominica ke sanar da yanke huldar diflomasiyya da Taiwan.

A cewar Wang Yi, amincewa da kasar Sin daya tak a duniya, tsari ne da al'ummomin kasashen duniya suka amince da shi, kuma shi ne tubalin da kasar Sin ke bukata na kulla hulda da wata kasa.

Miguel Vargas ya kara da cewa, wannan shi ne mataki mai muhimmanci, wanda kuma ya dace ga Jamhuriyar Domica, domin kulla huldar diflomasiyya da jamhuriyar al'ummar kasar Sin, inda ya ce a yanzu, Dominica za ta bi jerin kasashe 175 dake mara baya ga kuduri na 2758 na MDD.

Bugu da kari, ya ce Jamhuriyar Dominica ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan, ya na mai alkawarin cewa kasarsa, ba za ta kara hulda ko musayar bayanai a hukumance da Taiwan ba.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China