Kwamishinan wanda ke zantawa da 'yan jarida a Damaturu fadar mulkin jihar ta Yobe, albarkacin ranar yaki da cutar Malaria ta duniya ta bana, ya ce yara kanana da mata masu juna biyu su ne cutar ta fi gallazawa.
Ya ce duk da yiwuwar magance yaduwar wannan cuta a tsakanin al'ummar Najeriya, har yanzu tana ci gaba da kasancewa babban kalubale a fannin kiwon lafiyar kasar. An yiwa ranar ta bana taken "Shiri tsaf domin kauda Malaria".
Alkaluman kididdigar kula da lafiyar al'umma sun nuna cewa, Najeriyar ce ke kan gaba wajen fama da matsalolin da cutar ta malaria ke haifarwa, inda a duk shekara ake samun wadanda suka kamu da cutar kusan miliyan 51, kana tana hallaka kusam mutane 207,000. Adadin da ya kai kusan kaso 30 bisa dari na ta'annatin da wannan cuta ke yi a daukacin nahiyar Afirka. Kaza lika cutar na barazana ga kusan kaso 97 bisa dari na daukacin al'umma Najeriyar su miliyan 173.
Ana dai bikin ranar Malaria ta duniya ne a duk ranar 25 ga watan Afirilun ko wace shekara, a wani mataki na yunkurin lalubo hanyoyin dakile yaduwar cutar, bisa burin kaiwa ga ganin bayan ta a duniya baki daya.(Saminu Alhassan)




