in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon harin cocin Benue ya kai 16
2018-04-25 11:24:50 cri

'Yan sanda a jihar Benue dake tsakiyar Najeriya sun ce wasu mutane da ake zargin makiyaya ne, sun hallaka mutane 16 a wata majami'ar katolika dake kauyen Mbalon. Shugaban rundunar 'yan sandan jihar Owoseni Fatai ne ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Talata a birnin Makurdi fadar mulkin jihar.

Mr. Fatai ya ce maharan sun kutsa kai ne cikin majami'ar da sanyin safiyar ranar Talata suka kuma bude wuta kan masu ibada dake ciki. Fatai, wanda ya bayyana wannan lamari a matsayin abun takaici, ya ce 'yan sanda su lashi takobin cafkewa, tare da hukunta wadanda ke da hannu a aikata wannan ta'asa. Ya ce tuni suka fara gudanar da bincike game da wannan lamari, yayin da aka kara yawan 'yan sanda a yankin.

Da yake tsokaci game da wannan al'amari, gwamnan jihar ta Benue Samuel Ortom, ya ce bisa jimilla, yawan mutanen da makiyaya suka hallaka a jihar ya kai mutum 45.

Da fari dai an bayyana cewa, mutane 13 ne harin na ranar Talata ya rutsa da su, ciki hadda limaman cocin su 2.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da wannan hari, yana mai bayyana shi a matsayin tsantsar rashin imani.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China