Onyema Nwachukwu ya ce sojojin sun cimma wannan nasara ne, yayin wani aikin sintiri da suka gudanar a yankin Benisheikh dake jihar ta Borno. Kaza lika sojojin sun hallaka wani mayakin kungiyar daya, tare da kubutar da wani mutum guda da kungiyar ke tsare da shi. Jami'in ya ce sojojin sun samu bayanan sirri da suka taimaka masu wajen gano sansanin, a wani bangare na yunkurin da suke ci gaba da yi na raba daukacin jihar ta Borno da ayyukan 'yan ta'adda na Boko Haram.
Rahotanni sun bayyana cewa sai da sojojin suka yi musayar wuta da mayakan kungiyar kafin su kai ga cin lagon su. (Saminu Alhassan)