in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majlisar wakilan Nijeriya ta soki shugaban kasar game da sayen jiragen yaki daga Amurka
2018-04-25 11:33:24 cri

Majalisar wakilan Nijeriya, ta soki Shugaban Kasar Muhammadu Buhari, game da sayen jiragen yaki daga Amurka ba tare da amincewarta ba.

An samu suka da dama bayan shugaban majalisar ya karanta wasikar da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike musu, inda 'yan majalisar suka yi ta neman jin dalilin da ya sa shugaban ya bada umarnin fitar dala miliyan 496 domin sayen jiragen yaki ba tare da samun amincewar majalisar ba kamar yadda doka ta tanada.

Sai a shekarar 2020 Amurka za ta bada jiragen 12 samfurin Super Tucano, karkashin yarjeniyar da gwamnatocin biyu suka cimma. An dai shafe shekaru ana tattaunawa game da sayen jiragen.

Cikin wasikar da ya aikewa majalisar a jiya Talata, Shugaba Buhari ya ce an riga an samu sahalewar Amurka game da sayen jiragen, sai dai akwai wa'adin da aka diba na biyan wani bangare na kudin, wanda idan ba a cika ba, yarjejeniyar za ta rushe.

Shugaban ya roki majalisar ta sanya kudin dala miliyan 496, ya zama kari cikin kudurin kasafin kudin bana, yana mai jan hankalin 'yan majalisar game da matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa an biya kudin kai tsaye ga ma'aikatar baitulmalin Amurka, inda aka kuma shirya zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a ranar 30 ga watan nan na Afrilu.

'yan majalisar dai sun zargin shugaban kasar da take kundin tsarin mulki wanda ya tanadi yadda za a kashe kudin gwamnati bisa amincewar majalisar dokoki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China