in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka matukin jirgin Rasha bayan da 'yan tawayen Syria suka harbo jirgin saman a yankin Idlib
2018-02-04 13:24:21 cri
Wani matukin jirgin saman Rasha ya gamu da ajalinsa bayan da 'yan tawayen kasar Syria suka harbo jirgin saman a yankin arewa maso yammacin lardin Idlib a ranar Asabar.

A cewar hukumar sa'ido game da kare hakkin dan adam ta kasar Syria, bayan da jirgin saman yakin ya rikito kasa a yankin da aka kakkabo shi, matukin jirgin ya sauko kasa kuma nan take jirgin ya tarwatse inda ya fado kan 'yan tawayen wadanda suka yi yunkurin kwace jirgin.

Bugu da kari, wasu 'yan fafutuka sun wallafa hotunan wani mutum da suka yi ikirarin gawar matukin jirgin yakin kasar ta Rasha ne.

Gidan talabijin na British Sky News ya rawaito cewa, an yi amana wasu makamai masu linzami na Rasha ne suka yi sanadiyyar kakkabo jirgin yakin a gabar tekun Mediterranean, a yankin na Idlib.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da faduwar jirgin saman da kuma mutuwar matukin jirgin.

Kwana guda gabanin faruwar lamarin, wata majiya ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun sojin Syria suna gab da yankin Saraqeb, wajen da ya kasance a matsayin babban sansanin dakarun LLC masu alaka da kungiyar al-Qaida a lardin Idlib, bayan mummunan lugudan wuta da dakarun kasar Rashan masu samun goyon bayan dakarun Syriar suka kaddamar a yankin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China