Wannan ya biyo bayan wata sanarwar hadin gwiwa ne wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angel Merkel suka fitar, bayan wata tattaunawar da suka yi ta wayar tarho tsakaninsu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Macron da Merkel, sun bukaci Rashar da ta matsawa gwamnatin Syriar lamba don ganin ta dakatar da kaddamar da hare-haren boma bomai kan 'yan tawaye ba tare da bata lokaci ba, kana ta hanzarta aiwatar da yarjejeniyar da kwamitin sulhun MDD ya amince da shi a ranar Asabar, tare da aiwatar da kyakkyawan tsarin sanya ido kan yarjejeniyar, kamar yadda fadar shugaban kasar Faransa ta sanar. (Ahmad Fagam)