in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin saman fasinji na kasar Iran ya fadi
2018-02-19 13:09:39 cri

Gidan telebijin na kasar Iran ya tsamo labarin gwamnatin kasar a ranar 18 ga wata cewa, wani jirgin saman kasar Iran mai dauke da mutane 66 ya fadi a birnin Semirom a kan hanyarsa daga birnin Tehran, babban birnin kasar zuwa birnin Yasuj dake kudu maso yammacin kasar. Hukumar jiragen sama ta kasar Iran ta tabbatar da cewa, dukkan mutane 66 dake cikin jirgin saman sun rasu a sakamakon hadarin.

Shugaban cibiyar bada hidimar jinya cikin gaggawa ta kasar ya bayyana cewa, jirgin saman ya fadi ne a birnin Semirom dake jihar Isfahan ta tsakiyar kasar Iran, mai tazarar kilomita 185 daga birnin Yasuj.

Bisa labarin da gidan telebijin din kasar Iran ya bayar, an ce, masu ceto suna kan hanyar zuwa wurin da hadarin ya faru, amma wajen yanki ne mai duwatsu, kana akwai rashin kyawun yanayi, don haka abu ne mai wuya a iya gudanar da aikin ceton.

Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya nuna rashin jin dadi ga hadarin, kana ya jajantawa iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin tare da gwamnatin kasar Iran da jama'arta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China