in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kira da a kiyaye yarjejeniyar nukiliyar Iran
2018-01-18 10:16:34 cri

A yayin da aka cika shekaru biyu da aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran, a jiya Laraba, Mr. António Guterres, babban sakataren MDD ya bayar da sanarwa ta hannun kakakinsa Stephane Dujarric, inda ya yi kira da a martaba yarjejeniyar.

Sanarwar ta ce, babban sakataren yana da imanin cewa, yarjejeniyar nukiliyar Iran ita ce hanya mafi dacewa ta tabbatar da amfanin shirin nukiliyar Iran ta bangaren kiyaye zaman lafiya, wadda babbar nasara ce da aka cimma a bangaren diplomasiyya na hana yaduwar makaman nukiliya, wadda kuma ta taimaka matuka wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro a shiyyar da ma duniya baki daya. Babban sakataren ya kuma lura da cewa, hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta sha tabbatar da yadda Iran ta cika alkawuran da ta dauka game da yarjejeniyar.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, babban sakataren ya yi kira da a daidaita matsalolin da suka shafi batun aiwatar da yarjejeniyar bisa tsarin da yarjejeniyar ta tanada.

A ranar 12 ga wata ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, zai tsawaita wa'adin kawar da takunkumin da aka sanya wa Iran, sai dai wannan shi ne karo na karshe, ya kuma bukaci a yi wa yarjejeniyar gyaran fuskan da ya shafi kara karfin kayyade harkokin makamai masu linzami na Iran. A cewarsa, idan ba a kai ga cimma yarjejeniyar kamar yadda ya bukata ba, hakika, kasar Amurka za ta fice daga yarjejeniyar. Sai dai Iran a nata bangaren ta bayyana cewa, ba za ta sake shiga shawarwari game da yarjejeniyar ba. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China