in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kammala shirin bada tallafi na dala miliyan 1 ga 'yan gudun hijirar Iran
2018-02-14 11:19:23 cri

Jiya Talata, Ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Iran ya sanya hannu kan shedar shirin hukumar samar da abinci ta MDD (WFP), bayan da kasar ta samu nasarar kammala shirin tallafawa 'yan gudun hijirar na dalar Amurka miliyan guda.

Karkashin yarjejeniyar shirin wanda ta kulla da WFP a watan Agustan 2017, gwamnatin kasar Sin ta samar da gudunmowar dala miliyan 1 ga shirin na WFP, domin sayen abinci ga 'yan gudun hijirar Iran, wadanda galibinsu suka fito ne daga kasashen Afghanistan da Iraqi.

Jakadan kasar Sin a Iran Pang Sen, wanda ya halarci bikin a madadin gwanatin kasar Sin ya bayyana cewa, ko da yake kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, amma har yanzu kasa ce mai tasowa, idan aka yi la'akari da karfin ma'aunin tattalin arzikinta na GDP.

Ya ce kasar Sin a shirye take ta cigaba da bada taimako ga kasashe masu tasowa gwargwadon karfinta, musamman ma kasashe mafiya koma bayan cigaba domin yakar talauci.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China