An kulla yarjejeniyoyin ne a lokacin gudanar da taron hadin gwiwar kyautata mu'amala na Morocco-Nijer karo na 4, wanda ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita, da takwaransa na Nijer Ibrahim Yacoubou suka jagoranta.
Yarjejeniyar ta shafi bangarori da dama, da suka hada da tattalin arziki, sufuri, kiwon lafiya, shari'a, yawon bude ido da raya al'adu.
Da yake jawabi a lokacin ganawar, Bourita ya yaba da irin rawar da jamhuriyar Nijer ta taka wajen kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaron yankin Sahel, ya kuma bayyana irin karuwar kalubalen tsaro dake addabar yankin na Sahel.
Yacoubou ya yabawa Morocco bisa yadda take ci gaba da nuna goyon baya ga Nijer, kana ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu da cewa tamkar abin koyi ne a nahiyar Afrika, kuma bangare ne na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Haka zalika ya yabawa kasar Morocco sakamakon matakin da ta dauka na sake zama mamba a kungiyar tarayyar Afrika (AU), ya ce wannan babban abin alfahari ne ga kungiyar ta Afrika.
Ministan harkokin wajen na Nijer ya kuma nuna goyon bayansa ga bukatar da kasar Morocco ta nema na shiga kungiyar ECOWAS. (Ahmad Fagam)