in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da hada hannu da kasashen Rasha da Indiya don tabbatar da zaman lafiya a duniya
2017-12-12 11:39:58 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce ya kamata kasar Sin da Rasha da Indiya su taka muhimmiyar rawa a yayin sauyin tsarin duniya da tabbatar da zaman lafiya.

Wang Yi ya bayyana haka ne a jiya, yayin taro na 15, na ministocin harkokin wajen kasasehen 3.

Ya ce hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Rasha da Indiya ya biyo bayan bunkasuwar kasashen duniya da kuma dangantakar demokradiyya tsakanin kasa da kasa, wanda ya ce na da nufin neman cimma burin kasashen uku da yankinsu da ma duniya baki daya.

A nasu bangaren, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavro da takwaransa na Indiya Susma Swaraj, sun ce la'akari da halin sarkakkiya da duniya ke cikin yanzu, akwai bukatar kasashen uku su kara inganta hadin gwiwa da magance rikicin yanki da raya tattalin arziki da yaki da ta'addanci da sauyin yanayi da aiwatar da manufofin muradun karni masu dorewa da sauransu, bisa tsarin hadin gwiwar kasa da kasa irin na MDD da kungiyar G20 da BRICS da SCO, domin matsa kaimi wajen kafa wata duniya mai adalci da tsarin demokradiyya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China