Madam Hua ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka yi a yau Talata, inda ta kara da cewa, kasar Sin ta dade tana raya manyan ayyukan more rayuwa a Dong Lang, ciki har da gina hanyoyi, don biyan bukatun tsaro da kyautata zaman rayuwar sojoji da jama'a dake zaune a yankin. Ta kara da cewa, Sin za ta yi la'akari da yanayi da kuma sauran fannoni, don tsara manufofi na raya yankin. (Bilkisu)