Modi ya taya wa Xi Jinping murnar zama shugaban kasar Sin, ya ce, samun zarcewa da shugaba Xi Jinping ya yi ya shaida cewa jama'ar kasar Sin suna nuna masa goyon baya.
Shugaba Xi Jinping ya nuna godiya ga Modi bisa taya shi murnar lashe zaben. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, an samu nasara kan manyan taruka biyu da kasar Sin ta gudanar wato taron NPC da na CPPCC, inda aka zabi sabbin shugabannin hukumomin kasar da na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar, da zartas da gyaran kundin tsarin mulkin kasar da sauran manyan daftari, da kuma fara yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwar kasar. Kasar Sin za ta kara yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje don sa kaimi ga samun bunkasuwa tare da sauran kasashen duniya yayin da take kokarin samun bunkasuwar kanta. (Zainab)