Wu Qian ya bayyana cewa, zaman lafiya a kan yankin dake tsakanin Sin da Indiya shi ne zaman lafiyar yankin baki daya, wanda ya dace da moriyar kasashen biyu da jama'arsu. Sin ta yi kashedi ga kasar Indiya cewa, ya kamata ta koyi darasi daga wannan batun, da martaba yarjejeniyar iyakar kasa da kasa, da ka'idojin dokokin kasa da kasa, da hada kai tare da kasar Sin wajen tabbatar da zaman lafiya a kan iyakar da ke kasashen biyu, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu. Wu Qian ya kara da cewa, sojojin Sin sun yi imani tare da tabbatar da 'yancin mallakar kasar, da tsaron kasar, da kuma moriyar bunkasuwar kasar, da ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya gaba daya. (Zainab Zhang)