in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya ce kasar Sin muhimmiyar ginshiki ce ga ayyukan wanzar da zaman lafiya
2018-04-06 12:57:42 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce a yau, kasar Sin ta zama muhimmiyar ginshiki ga ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Antonio Guterres ya bayyana a jiya cewa, a yanzu, kasar Sin ita ce kasa ta 2 da ta fi bada gudummuwar kudi ga ayyukan wanzar da zaman lafiya, kuma tana daya daga cikin kasashen da ke da adadi mai yawa na jami'an wanzar da zaman lafiya da ake da su.

Ya kara da cewa, akwai 'yan sandan kasar Sin da jami'an wanzar da zaman lafiya 2,400 dake aiki a kasashe 14, yana mai cewa akwai jajircewa mai karfi ta fuskar wanzar da zaman lafiya daga kasar Sin.

Da yake ganawa da manema labaran kasar Sin kafin bulaguronsa zuwa kasar domin halartar taron BO'AO na nahiyar Asiya, ya ce suna ganin irin rawar da kasar Sin ke takawa, ba kadai ta hanyar bada gudummawar dakaru ba, har ma da gudummawa game da tattaunawar da za a yi a bana kan yadda za a inganta ayyukan wanzar da zaman lafiya, ta yadda ayyukan za su kara samun alkibla da kuma kare jami'ansa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China