in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yabawa gudunmawar da MDD ke bayarwa wajen kiyaye zaman lafiya da na karko
2018-04-20 15:51:31 cri

Zaunannen wakilin Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana a jiya Alhamis cewa, Sin na yabawa sosai ga gudunmawar da Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Laberiya ya aiwatar wajen kiyaye zaman lafiya da na karko. Kuma ya yi imanin cewa, gwamnati da jama'ar Laberiya zasu cigaba da raya kasa da tattalin arziki cikin hadin gwiwa a nan gaba.

A gun taron da MDD ta yi a wannan rana, Wu Haitao ya ce, shirin wanzar da zaman lafiya muhimmin mataki ne na kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya. Sin ta kan nace ga daidaita shirin da rundunar zata dauka bisa hakikanin halin da ake ciki a wasu kasashe har zuwa lokacin janye jikinsu daga kasar. Ya kamata a mutunta burin wadannan kasashe tare da kara sulhunta kasashe da yankuna masu ruwa da tsaki.

Ban da wanann kuma Wu Haitao ya yi kira ga kasashen duniya dasu ci gaba da hada kai da kasar don bada taimako wajen raya tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China