in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci
2018-04-18 10:26:37 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce a shirye kasar Sin take ta dauki matakan kariya, idan Amurka ta ci gaba da yin barazana ga huldar kasa da kasa da na cinikayya.

Hua Chunying wadda ta bayyana haka yayin taron manema labarai da aka saba yi, ta ce kasar Sin ta sha bayyana matsayarta, inda ta ce, ya kamata kasar da Amurka, su mutunta tare da tafiyar da juna bisa daidaito da moriyar juna.

A cewar kakakin, yayin da suke tattaunawa da kasar Sin a 'yan kwanakin da suka gabata, Japan da India, su ma sun bayyana goyon bayansu ga tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa da kuma cinikayya cikin 'yanci a duniya, karkashin ka'idojin kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO. Inda ta ce ra'ayin na su ya yi daidai da na galibin kasashen duniya.

A martaninta game da sakon da shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce Rasha da Sin na rage darajar kudadensu, Hua Chunying ta ce, kasar Sin ta gano wani rahoto da ma'aikatar baitulmalin Amurka ta fitar, inda ta ce babu wata abokiyar huldar kasar dake sauya farashin musayar kudadenta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China