in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron ciniki ta internet na duniya na shekarar 2018
2018-04-15 17:43:16 cri
An kammala taron ciniki ta internet na duniya na shekarar 2018 a birnin Yiwu na lardin Zhejiang a ranar 13 ga wata.

Taken taron na wannan karo shine "Yin kirkira a duniya da kyautata yanayi na nan gaba", za a yi jawabai kimanin 29, da yin shawarwari sau 4, wadanda zasu shafi fannonin fasahohin zamani, sabbin hanyoyin saye da sayarwa, da ciniki ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani, da ciniki tsakanin kasa da kasa, da cinikin aikin gona ta internet da sauransu.

Daraktan gudanarwa na kwamitin ciniki ta internet na kasar Sin Su Jun ya yi jawabi a yayin taron inda ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun zama manyan kasashen dake jagorantar harkokin ciniki ta yanar gizo a duniya a halin yanzu. Ana bunkasa harkokin ciniki ta internet a kasar Sin yadda ya kamata, wadda ta zama abin misali ga duniya ta wannan fanni.

Wakilai daga kamfanin JD na kasar Sin, da kamfanin Mi na kasar Sin, da kungiyar ciniki ta internet dake tsakanin kasa da kasa ta kasar Rasha, da kungiyar ciniki ta internet ta kasar Jamus, da kamfanin Tradeindia na kasar Indiya, da kamfanin YEATrade na kasar Chile da sauran kamfanonin ciniki ta internet na kasashe da yankuna 15 wadanda yawansu ya zarce dubu daya ne suka halarci taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China