in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi shawarwari da Kim Jung Un
2018-03-28 09:35:28 cri


Bisa gayyatar da babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, Xi Jinping ya yi masa, shugaban jam'iyyar kwadago ta Koriya ta arewa, kuma shugaban majalisar kula da harkokin kasa Kim Jung Un ya kawo ziyara kasar Sin ba a hukumance ba a tsakanin ranakun 25 da 28 ga watan Maris.

A lokacin da yake ziyara a kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya yi shawarwari da Mr. Kim Jung-Un, sannan babban sakatare Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan sun shiryawa Kim Jung-Un da uwargidansa Ri Sol Ju, liyafa kana har ma sun jagorancesu zuwa kallon wasannin kwaikwayo.

Mr. Li Keqiang, mamba dindindin na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma firaministan gwamnatin kasar, da Mr. Wang Huning, mamba dindindin na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren ofishin sakatariyar kwamitin kolin jam'iyyar, da kuma mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan bi da bi sun halarci wasu bukukuwa.

A yayin ganawar, a madadin kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya nuna maraba da ziyararsa ta farko da Kim Jung Un ya kawo kasar Sin. Xi Jinping ya bayyana cewa, ya kawowa kasar Sin wannan ziyara a wani lokaci na musamman, ya bayyana cewa, ziyarar tana da muhimmmanci sosai, ya kuma alamta cewa, mista Kim da kwamitin kolin jam'iyyar kwadago ta Koriya ta arewa suna maida hankali sosai kan huldar dake tsakanin jam'iyyun siyasa na kasashen biyu, da kuma tsakanin kasashen biyu, mun gamsu da matakinka inji shugaba Xi.

A nasa bangaren, Kim Jung Un ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan, kasar Sin tana da albishiri iri iri. A bara, jam'iyyar kwaminis ta kasar Si ta shirya babban taron wakilanta karo na 19 cikin nasara, sannan a kwanan baya, kun samu nasarar shirya taruka biyu. Shugaba Xi Jinping ya samu amincewa da goyon baya matuka daga al'ummomin kasa gaba daya. Bisa al'adar dake tsakanin kasashen Koriya ta arewa da Sin, ya kamata in zo kasar Sin in taya ka murna a gabanka. Yanzu, halin da ake ciki a yankin Koriya ya hanzarta samun ci gaba da wasu muhimman sauye-sauye, bisa zumunci da amincin dake tsakaninmu, ya kamata in zo kasar Sin in sanar maka halin da ake ciki yanzu.

Xi Jinping ya jaddada cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatinta na maida hankali sosai kan huldar hadin gwiwa irin ta sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Koriya ta arewa. Kiyayewa da karfafawa da kuma kara bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu itace babbar manufar da jam'iyyar kasar Sin da gwamnatinta suke tsayawa kai. Sannan Xi Jinping ya bayar da ra'ayoyinsa hudu kan yadda za a ci gaba da bunkasa huldar dake tsakanin kasashen Sin da Koriya ta arewa cikin dogon lokaci mai zuwa yadda ya kamata.

Sannan, shugabannin biyu sun kuma yi musayar ra'ayoyinsu kan halin da ake ciki a tsakanin kasa da kasa, kuma a yankin Koriya ta arewa.

Xi Jinping ya nuna cewa, bayan an shiga shekarar bana, halin da ake ciki a yankin Koriya ya samu kyawawan sauye-sauye sakamakon muhimmin kokarin da bangaren Koriya ta arewa ya nuna. Mun gamsu da kokarinku. A batun yankin Koriya ta arewa kuwa, muna tsayawa kan cimma burin hana kasancewar sinadaren nukiliya, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, sannan ya kamata a daidaita batutuwa ta hanyar yin shawarwari. Muna kiran bangarori daban daban dasu nuna goyon baya ga kokarin kyautata huldar dake kasancewa tsakanin bangaren arewa da na kudu na yankin Koriya, ta yadda za a iya bayar da kokari na a zo a gani wajen ingiza yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a yankin. Bangaren Sin yana son ci gaba da taka rawarsa mai dacewa kan batun yankin Koriya. Yana kuma bayar da kokarinsa tare da sauran bangarori, ciki har da bangaren Koriya ta arewa domin kokarin sassauta halin da ake ciki a yankin.

A nasa bangaren, Kim Jung Un ya bayyana cewa, yanzu halin da ake ciki a yankin Koriya na samun kyautatuwa a kai a kai. Mun dauki matakan sassauta hali mai tsanani a yankin, har ma mun bayar da shawararmu ta yin shawarwari cikin lumana. Bisa umarnin da marigayi shugaba Kim Il Sung da na marigayi babban sakatare Kim Jong Il suka bayar, muna namijin kokarin kawar da nukiliya daga yankin Koriya, wannan ne matsayin da muke bi, kuma ba zamu canja ba har abada. Muna da niyyar mayar da huldar dake tsakanin bangarorin arewa da kudu zuwa huldar sulhu ta hadin gwiwa a tsakaninsu. Muna son shirya taron ganawa tsakanin shugabannin bangarorin arewa da kudu, da kuma yin shawarwari da bangaren Amurka, har ma shirya ganawa tsakanin shugabannin kasashen Koriya ta arewa da Amurka. Idan bangaren Koriya ta kudu da Amurka sun mayar da martani ga kokarinmu cikin sahihanci, har ma zasu iya kafa wani yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta hanyar daukar matakan shimfida zaman lafiya, za a iya daidaita batun kawar da nukiliya daga yankin Koriya. A lokacin da ake kokarin yin haka, muna fatan kara yin mu'amala bisa manufa tare da bangaren Sin, domin tabbatar da ganin an yi shawarwari da kuma kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Koriya.

Kafin a yi shawarwari, Xi Jinping ya shirya wani bikin maraba da zuwan Kim Jung Un a babban dakin taron al'ummar Sin na Beijing.

Wasu manyan shugabannin kasar Sin kamar Ding Xuexiang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren ofishin sakatariyar kwamitin kolin jam'iyyar, kana shugaban ofishin kula da harkokin yau da kullum na kwamitin kolin jam'iyyar, da Mr. Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da Mr. Guo Shengkun, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren ofishin sakatariyar kwamitin kolin jam'iyyar, kana sakatare mai kula da harkokin mulki da shari'a a kwamitin kolin jam'iyyar, da Mr. Huang Kunming, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren ofishin sakatariyar kwamitin kolin jam'iyyar, kana shugaban hukumar yayata labaru ta kwamitin kolin jam'iyyar, da Mr. Cai Qi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakatare mai kula da harkokin reshen birnin Beijing na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kuma Mr. Wang Yi, wakilin majalisar gudanarwa ta gwamnatin kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin da wasu mataimakan shugaban kwamitin kolin jam'iyyar kwadago ta Koriya ta arewa kamar su Choe Ryong Hae, da Mr. Pak Kwang Ho da Mr. Ri Su Yong da Mr. Kim Yong Chol da Ri Yong Ho sun kuma halarci bukukuwa iri iri. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China