Dangane da rikicin diplomasiyya a tsakanin kasashen Birtaniya da Rasha, yau Alhamis Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin na fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki za su bi diddigin batu su kuma bankado gaskiyar lamarin, kana su daidaita rikicin ta hanyar tattaunawa yadda ya kamata.
A 'yan kwanakin nan, rikicin diplomasiyya a tsakanin Birtaniya da Rasha sakamakon yunkurin hallaka tsohon dan leken asirin kasar Rasha mai cin tudu biyu Sergei Skripal a Birtaniya yana ci gaba da daukar wani salo. A yammancin jiya ne, kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa domin nazartar lamarin. (Tasallah Yuan)