in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falesdinu ta ki warware matsalarta ta wani daftarin wucin gadi
2018-03-08 10:07:19 cri
Kwamitin gudanarwa na kungiyar 'yantar da Falesdinu ya jaddada a jiya Laraba cewa, Falesdinun ta ki a yi amfani da daftarin wucin gadi wajen warware matsalar da take gamuwa da ita.

Cikin wani rahoton da aka fidda bayan taron kwamitin da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya jagoranta, wanda aka yi a birnin Ramallah dake yamamcin kogin Jordan, an bayyana cewa, a yayin taron yin nazari kan batun Falesdinu da kwamitin sulhu na MDD ya kira a ranar 20 ga watan Fabrairu, shugaba Abbas ya bukaci a yi wani taron kasa da kasa game da batun Falesdinu bisa dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin MDD da abin ya shafa, domin cimma buri na kafa kasar Falesdinu mai 'yancin kai, wadda za a mai da birnin Jerusalem ta Gabas a matsayin babban birnin kasar, yayin da za'a shata layi na yankin iyakar kasa bisa yadda aka yi a shekarar 1967. Wannan shi ne matsaya da kuma babban burin da Falesdinu za ta tsaya tsayin daka kansa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China