in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Palasdinu ta bukaci AL da OIC su kira taron gaggawa kan batun birnin Kudus
2017-12-04 09:55:21 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Palasdinu ta yi kira a gaggauta shirya taron kungiyar kasashen Larabawa da na kungiyar kasashen musulumi ta duniya (OIC) domin nuna adawa da matakan Isra'ila game da batun birnin Kudus.

Ministan harkokin wajen Palasdinu Riad Malki wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce, yanzu haka shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas yana tattaunawa da shugabannin kasashen duniya da dama game da abin da ka iya biyo baya game da yiyuwar shawarar Amurka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Isra'ila da kuma mayar da ofishin jakadancin Amurkar daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus. Baya ga matakin baya-bayan da wasu kungiyoyin Yahudawa ke dauka a cikin harabar masallacin Al-Aqsa.

A don haka gwamnatin hadin kan kasa ta Palasdinu ta bukaci gwamnatocin kasashen Larabwa da kasashen Muslumi da su kawo karshen kutsen da Yahudawa ke yi a harabar masallacin karkashin kariyar dakarun Isra'ila, matakin da mai magana da yawun gwamnatin Palasdinu Yousef Mahmoud, ya bayyana a matsayin keta hurumin Palasdinu, da dokokin kasa da kasa, da kuma hakkokin bil-Adama. Kuma hakan na iya wargaza shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, har ma yana iya sanadiyar barkewar wani sabon tashin hankali.

Wasu rahotanni daga Amurka ne suka bayyana cewa, mai yiwu a ranar Laraba shugaba Donald Trump na Amurkar ya sanar da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, duk da adawa da kasashen musulmi ke yi kan wannan mataki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China