Mahamat, ya taya Abiy Ahmed murnar tabbatar da shi a matsayin sabon firaministan kasar ta gabashin Afrika a ranar Litinin, inda kuma ya yaba da yadda aka sauya shugabancin kasar cikin lumana, kana ya bayyana matakin da cewa alamu ne dake nuna samun kyautatuwar siyasa a kasar Habashan.
Ahmed, wanda ya samu amincewar kafatanin 'yan majalisar wakilan kasar Habashan a matsayin sabon firaministan kasar a ranar Litinin, ya karbi ragamar shugabancin tun a jiya Litinin daga hannun tsohon firaministan kasar Hailemariam Desalegn, wanda ya yi murabus a ranar 15 ga watan Fabrairu bayan zanga-zanagar data barke a sassan kasar don kin jinin gwamnati.
Shugaban na AU ya yabawa tsohon firaiministan kasar bisa irin gudumowar da ya bayar wajen cigaban kasar Habasha da nahiyar Afrika baki daya.(Ahmad Fagam)