Sanarwar ta ce, bayan binciken da kungiyar ta yi a Duma a ranar 21 ga watan nan, a ranar 25 ga wata ta kara shiga garin, tare kuma da kai ziyara wani wurin na daban. An ce, za a debe burbushin shaidu da kwararru tawagar suka samu zuwa Rijswijk na lardin kudancin Holland, don a yi nazari a dakin gwaji da kungiyar OPCW ta amince da shi. Kaza lika kuma jami'an tsaron MDD, da gwamnatin Syria da kuma 'yan sandan Rasha sun ba da tabbaci ga tsaron tawagar jami'an dake aiki a Duma.
Baya ga haka, sanarwar ta ce, tawagar kasar Rasha ta sanarwa hukumar OPCW da cewa, za a shirya wani taro a ranar 27 ga wata a Hague dake lardin kudancin Holland, inda wasu 'yan kasar Syria za su bada shaidu game da zargin kai hari da makamai masu guba a Duma. (Bilkisu)