Xie Xiaoyan ya yi nuni da cewa, hanyar siyasa ce kadai ta dace a bi wajen daidaita batun Syria. Ya kuma kamata kasa da kasa su maida hankali ga bukatu, da fatan jama'ar kasar Syria. Su kuma kara kokari wajen gudanar da shawarwari na shimfida zaman lafiya, da sa kaimi ga bangarori daban daban wajen komawa shawarwarin warware matsalar kasar.
Game da batun makamai masu guba da aka yi zargin gwamnatin kasar da amfani da su kan fararen hula a Syria, Xie Xiaoyan ya yi nuni da cewa, ya kamata a yi bincike kan batun cikin adalci a dukkan fannoni. Ya ce, ya kamata MDD ta nada ma'aikatan binciken, kuma ya dace su fito daga sassa daban daban. Kana a samu cikakkun shaidu kafin a gabatar da sakamakon binciken. (Zainab)