Bisa sanarwar da fadar shugaban kasar Faransa ta bayar, yayin tattaunawar shugabannin biyu, Macron ya yi nuni da cewa, kasar Faransa tana fatan kara yin shawarwari tare da dukkan kasashen da batun Syria ya shafa, don kaddamar da wani yunkurin warware takaddamar su ta hanyar siyasa mai dorewa, tare da kara gudanar da ayyukan jin kai.
Sanarwar ta bayyana cewa, shugaba Macron ya jaddada fatansa, na yin shawarwari tare da kasar Rasha biyowa bayan aniyar da shugabannin kasashen biyu suka ayyana ta gudanar da mu'amala kan batutuwan dake shafar kasashen biyu, da ma na duniya baki daya, yayin da shugaba Macron ya kai ziyara a kasar Rasha a watan Mayu na bana. (Zainab)