Hakan dai ta samu yabo sosai daga kasa da kasa. Amma, sakamakon bincike mai lambar 301 da kasar Amurka ta yi, bai nuna hakikanin hali da kasar ke ciki ba wajen karfafa kiyaye ikon mallakar fasaha.
Shen ya ce, masana da kafofin watsa labaru a fannin na kasar Amurka su ma sun bayyana cewa, makin da Sin ta samu game da halin da take ciki na kiyaye ikon mallakar fasaha yana gaba a tsakanin kasashe masu samun matsakaicin kudin shiga.
Baya ga haka, Shen ya nuna cewa, ko da yaushe kasar Sin na bin ka'idojin cinikayyar kasa da kasa, wajen biyan kudi game da amfani da ikon mallakar fasaha. Yawan kudin da kasar Sin ta biya ga kasashen ketare a fannin ya wuce dallar Amurka biliyan 28.6, wato jimillar kudin ta wuce dalla biliyan 20, ciki kuwa yawan kudin da ta biya ga Amurka ya karu da kashi 14 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. (Bilkisu)