Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce, a halin yanzu, ana ci gaba da sabunta fasahohin sadarwa na zamani bisa fannoni daban daban, domin inganta zaman takewar al'umma da habaka tsarin gudanarwar ayyukan kasa ta fasahohin zamani da kuma biyan bukatun al'ummomin kasa ta yadda za su kara jin dadin zaman rayuwarsu.
Haka kuma, ya ce, a yayin taron mai taken "Raya harkokin sadarwa domin inganta fasahohin zamani, da kuma gaggauta aikin gina fasahohin zamani a kasar Sin", za a nuna manyan sakamakon da aka samu a fannonin habaka ayyukan gudanarwa ta hanyar amfani da fasahohin intanet da kuma raya tattalin arziki ta hanyar amfani da fasahohin zamani. Har ila yau, za a yi musayar ra'ayi kan bunkasa fasahohin zamani a kasar Sin, domin cimma ra'ayi daya da kuma sa kaimi ga bangarori daban daban na kasar Sin da su zurfafa amfani da fasahohin sadarwa na zamani ta yadda za a ba da karin tallafi ga al'ummar kasa da ba da gudummawa kan bunkasa zaman takewar su baki daya. (Maryam)